Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sace mutane 4 a yankin tsakiyar Nijeriya
2019-09-11 09:11:24        cri
'Yan sandan Nijeriya, sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace wasu mutane hudu yayin da suke bulaguro a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja dake yankin tsakiyar kasar a karshen makon da ya gabata.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya shaidawa manema labarai cewa wani gungun masu dauke da makamai sanye da kakin soji, sun tsayar da wata motar bus a kauyen Rijana dake kan hanyar, inda suka arce da fasinjoji 6 cikin daji.

Yakubu Sabo ya ce bayan samun kiran neman dauki, nan da nan 'yan sandan dake sintiri a yankin suka bi sahun barayin tare da bata-kashi da su, lamarin da ya kai ga ceto mutane 2. Yana mai cewa, barayin sun tafi da mutane 4.

Kakakin ya ce ana ci gaba da kokarin ceto sauran mutanen 4 tare da cafke barayin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China