Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe mutane 4 a kudancin Najeriya
2019-08-27 10:08:15        cri
Wasu 'yan bindiga da ba'a tantance ko su wanene ba da safiyar Litinin sun kashe 'yan sanda biyu da fararen hula biyu bayan da suka bude wuta a yankin Ikpoba-Okha dake jahar Edo, a kudancin Najeriya.

A cewar hukumar 'yandan shiyyar, 'yan bindigar sun bude wuta ne kan ayarin babban daraktan lafiya na wani asibitin yankin, inda suka hallaka 'yan sanda biyu dake tsaron jami'in lafiyar, kakakin hukumar 'yan sandan jahar Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin ga taron manema labarai da aka gudanar a Benin city, babban birnin jahar.

Mutane biyun da aka kashe a cikin tawagar, kawo yanzu ba'a tantance su ba, a cewar kakakin 'yan sandan.

Nwabuzor ya ce, maharan sun yi awon gaba da daraktan lafiyar bayan kaddamar da harin. Wata majiya daga yankin ta ce, 'yan bindigar su shida ne, amma kawo yanzu ba su sanar da neman kudin fansa ba tun bayan da suka dauke daraktan lafiyar zuwa wajen da ba'a sani ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China