Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a baiwa injiniyoyin Najeriya 60 horo a kasar Sin
2019-08-29 10:37:56        cri
Jami'in Najeriya ya ce kimanin injiniyoyin kasar sittin ne suka bar kasar zuwa kasar Sin, inda za su halarci shirin samun horo a fannin kera na'urorin samar da wutar lantarki.

Tawagar wacce ta tashi daga kasar ta yammacin Afrika a ranar Talata, za ta kasance a kasar Sin domin halartar horo na musamman na tsawon watanni 4, Olusegun Ayeoyenikan, kakakin hukumar kimiyya da fasahar samar da kayayyakin more rayuwa ta kasa (NASENI), ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Sanarwar ta kara da cewa, an tsara shirin ba da horon ne da nufin baiwa 'yan kasar cikakken ilmin kera na'urar samar da hasken wutar lantarki inda za'a dinga kerawa da kuma tafiyar da ayyukan na'urar a cikin kasar ta Najeriya, don baiwa 'yan kasar damar kerawa da kansu.

Ya ce wannan wani muhimmin shiri ne wanda gwamnatin kasar ta bullo da shi da nufin kafa kamfanin kera na'urar bada wutar lantarkin da kuma dakin gwaje-gwajen duba karfin wutar lantarkin a Najeriya.

A cewarsa, idan injiniyoyin suka kammala halartar shirin samun horon, za su koma gida Najeriya inda za su yi amfani da kwarewarsu a fannoni daban daban da suka samu daga kasar Sin game da yadda za su hada na'urar lantarkin da kula da na'urar a cibiyoyin gwaje-gwajen. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China