Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF: Yara miliyan 19 ne ba su da rejista a Nijeriya
2019-08-27 09:31:18        cri
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce adadin yaran da ba su da rejistar haihuwa a Nijeriya ya kai miliyan 19, lamarin da ya kasance abun damuwa dake tattare da matsaloli da dama a kasar.

Babbar jami'a mai kula da bada kariya ta asusun, Sharon Oladiji, ta ce daga cikin matsalolin rashin rejistar haihuwa, akwai tsare tsare da-ka, da gazawa wajen samar da bayanai game da lafiyar al'umma da kiyasin kasa da kuma tsare tsare yawan al'umma.

Jami'ar ta shaidawa manema labarai a jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar cewa, Nijeriya ita ce ke bin sahun kasar Indiya wadda ke da yara miliyan 71 marasa rejista, daga cikin kasashe 10 dake da adadi mafi yawa na yara marasa rejistar haihuwa a duniya.

Ta ce yaran da matsalar ta fi shafa a Nijeriya, sun fito ne daga gidaje iyaye matalauta da wadanda ba su yi karatu ba da na yankunan karka da kuma wurare masu nisan isa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China