Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka mutu a hadarin tankar mai a Najeriya ya karu zuwa 6
2019-09-05 11:29:33        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane shida ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu takwas kuma suka ji mummunan rauni, bayan da wata motar dakon mai ta yi bindiga a yankin tsakiyar kasar.

Hadarin ya faru ne ranar Jumma'ar da ta gabata a kan babbar hanyar Abuja-Kaduna, inda ya rutsa da mutane 14. Da farko an ba da rahoton mutuwar mutane uku.

Shugaban sashen kula da bala'u na hukumar ba da agajin gaggawa dake jihar Niger a yankin arewa maso tsakiyar kasar, Ahmed Inga ya bayyana cewa, uku daga cikin wadanda suka ji rauni sun mutu ranar talata, yayin da ake yi musu jinya sakamakom mummunan kunar da suka samu, bayan da motar ta yi bindiga.

Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa, direban motar ya arce yayin da motar ta yi bindiga, ta kuma haddasa wannan barna. Har yanzu ba a gano asalin direban da ma na mai motar ba.

Sai dai kuma, ana farautarsu, yayin da 'yan sanda ke gudanar da bincike don gano musabbabin hadarin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China