Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sandan Najeriya sun tabbatar da sace dan majalissar jihar Sokoto
2019-08-23 11:02:30        cri
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun yi awon gaba da dan majalissar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar karamar hukumar Dange-Shuni Aminu Bodai, bayan da suka kai farmaki gidansa da sanyin safiyar jiya Alhamis.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Abubakar Sadiq, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, rundunar ta aike da wasu jami'an ta domin su shiga farautar bata garin.

Kaza lika rundunar na gudanar da binciken kwakwaf a dajin dake daura da kauyen Bodai, da ma sauran yankuna masu makwaftaka da inda lamarin ya auku. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China