Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Barkewar zazzabin shawara ya yi sanadin mutuwar mutane 7 a Nijeriya
2019-09-07 16:40:08        cri
An tabbatar da mutuwar mutane 7 sanadiyyar barkewar zazzabin shawara a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, ta bayyana a jiya cewa, ta samu rahoton bullar zazzabin a jihohin Bauchi da Borno na yankin, a ranar 29 ga watan Augusta.

Shugaban cibiyar, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, mutum na farko da ya kamu da cutar dan jihar Bauchi ne da ya ziyarci wajen yawon shakatawa na Yankari tare da mahaifinsa a watan da ya gabata.

Sanarwar ta ce yayin da yaron ke samun kulawa, mahaifinsa ya mutu da irin alamomin zazzabin tun kafin a kai ga yin gwaji da samun sakamako.

A kuma ranar 3 ga watan Satumba ne aka tabbatar da mutuwar dalibai 6 na kwalejin ilimi ta jihar Borno, bayan alamomin zazzzabin na shawara sun bayyana a tare da su. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China