Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Hongkong ta yi Allah wadai da matakin nuna karfin tuwo da masu bore suka dauka
2019-09-07 16:22:04        cri

Safiyar yau Asabar, mai magana da yawun gwamnatin yankin musamman na Hongkong, ya yi Allah wadai da kakkausar murya, da matakin nuna karfin tuwo da masu bore suka dauka jiya a Prince Edward da Mong Kok da Yau Ma Tei da dai sauran wurare dake kewaye.

Jami'in ya ce, tun da yammacin jiya, masu tsattsauran ra'yi suka yi gangami a wadannan wurare don kai hari kan ofisoshin 'yan sanda da lalata kayayyakin gwamnati da tashar jirgin kasa ta MTR, tare da kunna wuta a wurare da dama. Yana mai cewa matakan da suka dauka sun keta doka tare da haifar da babbar illa. Ya ce wadannan masu bore sun tada zaune tsaye, kuma matakan da suka dauka na kawo babbar illa ga kayayyakin more rayuwa da kuma keta hakkin sauran mazauna. Ya kara da cewa, kunna wuta a cibiyar yankin zai iya haifar da hadari matuka, abin da zai yi barazana ga lafiyar jama'a. Gwmantin ta yi Allah wadai da matakan da suka dauka da kakkausar murya. Yana mai cewa 'yan sanda za su hukunta su yadda ya kamata, don tabbatar da lafiya da hakkin mazauna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China