Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hong Kong ya fuskanci tashin hankali a daren jiya
2019-09-01 16:43:45        cri
Kakakin 'yan sandan yankin musamman na Hong Kong ya sanar cewa a daren jiya cewa, Hong Kong ya fuskanci mummunan tashin hankali, 'yan sa'o'i kadan bayan da masu bore suka cinna wuta a manyan titunan yankin, kana suka lalata wasu gine-ginen gwamnati, da haifar da cikas game da sha'anin sufuri a birnin.

Yu Hoi-kwan, babban jami'in sashen hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan yankin, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, tashin hankalin da masu boren suka tayar ya yi sanadiyyar katse harkoki a wasu wurare da dama na Hong Kong tun daga yammacin ranar Asabar.

Kimanin mutane 40 'yan sanda suka damke, a kokarin da suke wajen tabbatar da bin doka da oda, inda suka shafe daren Asabar har zuwa wayewar garin Lahadi, da nufin magance laifuka da suka hada da yin gangami ba bisa doka ba, da ayyukan bata gari dake lalata kayayyakin gwamnati, da kuma masu kai hare-hare kan 'yan sanda. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China