Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi Allah wadai da harin bam cikin wata mota da aka kaddamar a Libya
2019-08-11 15:15:38        cri
A jiya Asabar kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da babbar murya da harin bam da aka kaddamar cikin wata mota a birnin Benghazi na kasar Libya, inda ya hallaka jami'an MDD 3 tare da jikkata wasu da dama.

A wani taron gaggawa da aka kira game da halin da ake ciki a Libya, wanda aka nemi Faransa ta kira taron, Joanna Wronecka, jakadiyar kasar Poland a MDD, kana shugabar taron, ta karanta wasikar kwamitin MDDr inda mambobin suka yi Allah wadai tare da bayyana bacin ransu game da kaddamar da harin.

Ta ce a madadin mambobin kwamitin, MDD ta yi Allah wadai da kakkausar murya, kana ba za'a taba lamintar irin wannan mummunan harin da ake kaiwa kan jami'an MDD ba wanda ya hallaka rayuka a birnin Benghazin kasar Libya a wannan rana. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China