Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin:Duk wani yunkuri na wargaza yankin Hong Kong ba zai yi nasara ba
2019-07-12 20:30:28        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa matuka da yadda kasar Amurka take kutsa kai cikin harkokin yankin Hong Kong da ma harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma kasar Sin ta gabatarwa bangaren Amurka kokenta kan wannan batu a hukumance.

Geng ya bayyana hakan ne, yayin da yake mayar da martani kan wasu rahotanni dake cewa, mashawarcin Amurka kan harkokin tsaro John Bolton, da mataimakin shugaban kasar Mike Pence da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo sun gana da dan kasuwar Hong Kong Jimmy Lai a kwanakin nan game da daftarin dokar da yankin ke kokarin zastarwa.

Jami'in na kasar Sin ya ce, duk wani yunkuri na haddasa rudani da rashin zaman lafiya a Hong Kong ba zai samu goyon bayan Sinawa ba, ciki har da 'yan uwa mazauna yankin Hong Kong, kuma ba zai yi nasara ba. Haka kuma kasar Sin za ta kare muradunta, tsaro tare da tabbatar da zaman lafiya da makoma mai kyau a yankin musamman na Hong Kong, tana kuma Allah wadai da tsoma bakin ketare a harkokin cikin gidanta ta kowane fanni. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China