Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da tabbatar da harsunan mutanen asalin yankuna daban daban na duniya
2019-08-10 17:15:01        cri
Babban sakataren MDD António Guterres ya yi jawabi game da murnar ranar mutanen asalin yankuna daban daban na duniya, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su kara tabbatar da harsunan mutanen asalin yankuna daban daban na duniya don ci gaba da gadonsu har abada.

Babban taron MDD ne ya zartas da wani kuduri a shekarar 1994, inda aka kebe ranar 9 ga watan Agusta a matsayin ranar mutanen asali na yankuna daban daban na duniya, taken ranar a bana shi ne "harsunan mutanen asalin yakuna". Guterres ya yi jawabi a wannan rana cewa, akwai harsuna 6700 a duniya, yawancinsu su harsuna ne na mutanen asalin yankuna daban daban, wadanda suka wakilci al'adu daban daban, amma kimanin rabinsu suna fuskantar hadarin karewa.

Mataimakiyar sakataren janar din Amina Mohammed ta bayyana a wurin bikin murnar ranar cewa, mutanen asali na yankuna daban daban na duniya sun fuskanci matsalar wariya, wadda ta kawo barazana ga hanyoyin rayuwa da al'adunsu gaba daya, don haka tilas ne a kara yin kokarin tabbatar da hakkinsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China