![]() |
|
2019-08-23 10:24:43 cri |
Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasar FRSC, ta ce wasu mutane biyu kuma sun ji munanan raunuka, yayin hatsarin da ya auku tsakanin motar bus kirar Toyota mai dauke da fasinjoji da wata babbar mota dake tahowa ta daya bangaren, a kan babban titin Jebba zuwa Ilorin dake jihar.
Shugaban hukumar FRSC a jihar Usheme Eshiet, ya shaidawa manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar Kwara cewa, ya ce lamarin ya auku ne sanadiyyar gudun wuce sa'a da tukin ganganci.
Ya ce motocin sun yi karo ne yayin da suke tunkarar wata karkatacciyar kwana dake kan titin. Yana mai cewa, direbobin sun kasa sarrafa motocinsu yayin da suka isa kwanar, lamarin da ya jawo hatsarin.
Bisa rahoton shekara da hukumar FRSC ta fitar, an samu hadurran mota 9,383 a shekarar 2017, ciki har da munanan haddura 2,587 da suka yi sanadin rayuka 5,121. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China