Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afirka dake cikin AfCFTA da su fito da alkaluman kasuwancin kasashensu
2019-09-05 11:17:44        cri

Jami'ai daga hukumar MDD mai kula a tattalin arzikin Afirka (ECA) da kungiyar tarayyar Afirka (AU) sun yi kira ga kasashen Afirka, da su fito da alkaluman kasuwancin kasashen nahiyar, ta yadda za su ci gajiyar damammakin dake kunshe cikin yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka(AfCFTA),

Jami'an sun yi wannan kiran ne yayin taron da ya hallara masana daga kasashe da hukumomin nahiyar a birnin Addis Ababan kasar Habasha, inda za su yi nazari, su kuma fito da wani tsari game da daftarin alkaluman kasuwancin kasashen dake cikin yarjejeniyar AfCFTA.

Jami'in tsare-tsare na cibiyar manufofin cinikayyar Afirka a hukumar ECA David Luke, ya shaidawa taron masanan, muhimmancin alkaluman kasuwancin kasashen, ta yadda za su ci gajiyar damammakin dake cikin yarjejeniyar.

Luke ya ce, alkaluman za su kara taka muhimmiyar rawa, wajen fahimtar kalubalen da jagororin sassa masu zaman kansu da 'yan kasuwa a matakai daban-daban suke fuskanta, kana su bayyanawa masu tsara manufofi wadannan kalubale.

A farkon watan Yulin wannan shekara ce, aka kaddamar da yarjejeniyar ta AfCFTA a hukumance, a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, matakin da take tabbatar fara aiki da yarjejeniyar, wadda kasashen nahiyar 54 suka sanyawa hannu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China