2019-09-02 10:57:34 cri |
Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu David Mabuza yace, a cikin wannan watan, ya kamata a yayata sakonnin muhimmancin lafiyar 'yan sanda a dukkan lungu da sako na kasar.
A cewar Mabuza, manufar shirya gangamin shine, domin fadakar da al'umma muhimmancin yin hadin gwiwa tsakanin jami'an 'yan sanda da al'ummar kasar.
Yace a lokacin bikin tunawa da ranar 'yan sanda ta kasar Afrika ta kudu, wajibi ne a fahimci cewa hadin gwiwa tsakanin 'yan sanda da jama'a yana bukatar a karfafashi kuma dukkan 'yan kasa su tallafawa shirin.
Mabuza ya jaddada aniyar yin aiki tare da ministan 'yan sandan kasar Bheki Cele da nufin kakkabe ayyukan bata gari a fadin kasar.
Yace ta hanayar cikakken hadi gwiwa tsakanin 'yan sanda da al'ummar kasa ne za'a iya cimma nasarar samun zaman lafiya, da bin doka da oda, kana za'a kawo karshen yawan kashe jami'an 'yan sandan kasar.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China