Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da taron WEF kan Afirka
2019-09-05 11:04:49        cri
A jiya Laraba ne, aka kaddamar da taron dandalin tattalin arziki na duniya game da nahiyar Afirka (WEF), a wani mataki na taimakawa nahiyar kafa masana'antun da za su bunkasa, har ma su yi goyayya a kasuwannin duniya.

Da take karin haske kan lamarin, darektar sashen kula da harkokin Afirka a dandalin na WEF, Elsie Kanza, ta bayyana cewa, masana'antun Afirka su ne kashin bayan tattalin arzikin nahiyar, amma har kullum ruhi da albarkatu kadai, ba za su iya taimaka musu kaiwa ga nasara ba. Sannan a mafi yawan lokuta, kamfanonin kirkire-kirkire da aka kafa, ba sa kaiwa ko'ina, saboda karancin kudade ko wasu ka'idoji masu tsauri da aka gindaya.

Kanza ta ce, a nahiyar, da kusan a halin yanzu kaso biyu bisa uku na matasa miliyan 420 ba su da aikin yi, kirkire-kirkire da sabbin abubuwa na da muhimmanci wajen kara samar da aikin yi. Kana yayin da ake fama da karancin guraben aikin yi a nahiyar, babu wanda zai yi tunanin kafa masana'antu a nahiyar.

Jami'ar ta bayyana cewa, masana'antu a Afirka na aiki ne na sama da matsakaicin kaso 13 cikin 100 da aka yi kiyasi a duniya, amma rashin tallafi da muhimman kayayyakin more rayuwa, na nufin akwai tabbaci na kaso 14 cikin 100 cewa, masana'antu da aka kafa a nahiyar, ba za su kai labari ba, idan aka kwatanta da na sauran sassan duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China