Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru da masu tsara manufofin Afrika sun bukaci a sauya salon aiwatar da yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi
2019-08-30 10:48:34        cri

 

Masana da masu tsara manufofin ci gaba na Afrika, sun bukaci a sauya salo mai tafiyar hawainiya da ake amfani da shi wajen aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris game tunkarar matsalar sauyin yanayi.

Kwararrun da masu tsara dabarun ci gaban sun yi kiran ne a lokacin babban taron sauyin yanayi da ci gaban Afrika karo na takwas (CCDA-8), wanda ke gudana a halin yanzu a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, tsakanin 28 zuwa 30 ga wannan wata.

Babban taron na hadin gwiwa tsakanin kungiyar AU, da hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), da bankin raya ci gaban Afrika (AfDB), da kuma kungiyar gamayyar Afrika kan sauyin yanayi, an karkare taron da yin kira da babbar murya daga ministoci da masanan Afrika, inda suka nemi a sauya salon tsarin da ake amfani da shi a halin yanzu wajen aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China