Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kada Birtaniya ta yi fadin rai da kiran kanta "mai kiyaye Hong Kong"
2019-07-03 20:07:55        cri

A Yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya jaddada cewa, kasar Sin ta maido da ikon mulkin yankin Hong Kong a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997. Kuma kasar Sin tana kulawa da harkokin Hong Kong bisa kundin tsarin mulkin kasar, da kuma muhimman dokokin kasar.

Jami'in ya kara da cewa, ba ruwan kasar Birtaniya da yankin musamman na Hong Kong, kana ba ta da alhaki kan yankin na Hong Kong. Kullum Birtaniya kan kira kanta "mai kiyaye Hong Kong", wanda tamkar nuna fadin rai ne kawai, kuma wani mafarki ne maras tabbas.

Geng Shuang ya fadi hakan ne, yayin da ya musunta kalaman ministan harkokin wajen kasar Birtaniya Jeremy Hunt dangane da Hong Kong, a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. Geng Shuang ya sake nanata cewa, yankin Hong Kong, yankin musamman ne karkashin shugabancin jamhuriyar jama'ar Sin. Kaza lika harkokin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wadanda Sin ba ta yarda da duk wata kasa, ko hukuma, ko wani mutum ya tsoma baki a ciki ba. Ya ce Sin na fatan Birtaniya, musamman ma mista Hunt, zai daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, kasancewar ba zai kai ga cimma manufarsa ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China