Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon wakilin MDD na neman samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Somalia
2019-06-26 12:08:17        cri
Sabon manzon musammam na Sakatare Janar na MDD a Somalia James Swan, ya isa Mogadishu a jiya Talata, yana mai alkawarin neman hanyar samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a kasar dake kahon Afrika.

James Swan wanda kuma shi ne shugaban shirin agaji na MDD a Somalia, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Mogadishu cewa, yana farin cikin aiki da abokan hulda na ciki da wajen kasar, wajen samar da dawawwamen zaman lafiya da al'ummar Somalia suka cancanci samu.

Swan ya maye gurbin Haysom, wanda a farkon shekarar nan gwamnatin Somalia ta zarga da take wasu ka'idoji da kuma tsoma baki da gangan cikin harkokin cikin gidanta.

An nada James Swan dan Amurka ne a ranar 30 ga watan Mayu, kuma yana da gogewa dangane da harkokin kasashen kudu da hamadar Sahara.

Aikin da ya yi na farko a Somalia ya gudana ne shekaru 25 da suka gabata, inda ya kasance jami'in dake kula da harkokin siyasa na ofishin manzon musammam na Amurka da ke Somalia, daga shekarar 1994 zuwa 1996. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China