Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta samar da tallafin alluran rigakafin cutar Ebola 300 ga Uganda
2019-08-31 16:54:36        cri
Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO,ta sanar da samar da tallafin alluran rigakafin cutar Ebola guda dari uku ga kasar Uganda, a wani kokari na yin allurar rigakafin cutar ga mutanen da mai yiwuwa sun taba mu'amala da wata yarinya data kamu da cutar.

Wakilin WHO dake Uganda ya bayyana a wani taron manema labarai a jiya Jumma'a cewa, wata 'yar kasar Kongo(Kinshasa) mai shekaru tara ta rasa ranta sakamakon cutar Ebola a ranar Jumma'a, don haka za'a yi alluran rigakafin da WHO ta samar ga mutanen da suka taba mu'amala da marigayiyar. A halin yanzu WHO na kokarin binciko mutanen da suka taba mu'amala da ita, musamman wadanda suka fi fuskantar barazana, ciki har da likitoci da nas-nas gami da ma'aikatan kwastam.

Yarinyar ita ce mutum na hudu da ya kamu da cutar ta Ebola a kasar Uganda tun bayan sabon zagayen barkewar cutar a Kongo(Kinshasa). A watan Yunin bana, an tabbatar da gano mutane uku wadanda suka kamu da cutar Ebola a Uganda, wadanda dukkansu daga Kongo(Kinshasa) suke.

Har wa yau, ma'aikatar kiwon lafiya ta Kongo(Kinshasa) ta sanar da cewa, tun bayan sabon barkewar cutar Ebola a kasar a watan Agustan bara kawo yanzu, adadin mutanen da aka gano sun kamu da ita ya zarce dubu uku, ciki har da sama da dubu biyu wadanda suka riga mu gidan gaskiya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China