![]() |
|
2019-07-23 11:10:20 cri |
Mahukuntan kasar Sin da na kasar Masar, sun amince da wata yarjejeniya, wadda ta shafi samar da kayayyakin koyar da ilimin fasahohi da sana'a, ga cibiyar horaswa ta Sin da Masar dake jami'ar Suez.
Ministar ma'aikatar zuba jari da hadin gwiwar kasa da kasa ta Masar Sahar Nasr ce ta sanya hannu kan takardar yarjejeniyar a madadin gwamnatin Masar, yayin da jakadan Sin a kasar Liao Liqiang ya wakilci gwamnatin Sin.
Yayin bikin sanya hannun, Nasr ta ce tsarin hadin gwiwa da sassan biyu ke da shi abun misali ne a fannin samar da horo ga dalibai masu koyon sana'o'i. Ta ce yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a jiya Litinin, ta dace da kudurin shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, game da bunkasa ilimin fasahohi, da koyon sana'a a daukacin matakan ilimin kasar, ta yadda matasa za su samu guraben ayyukan yi bayan kammala karatunsu.
A nasa bangare kuwa, jakada Liao cewa ya yi, sashen karatu na hadin gwiwa Masar da Sin, salon hadin gwiwa ne irin sa na farko tsakanin kasashen biyu, wanda ya maida hankali sosai ga horas da dalibai ilimin sana'o'i. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China