Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FIFA ta haramtawa Samson Siasia shiga harkokin wasan kwallon kafa har abada
2019-08-17 20:07:11        cri
Hukumar wasannin kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramtawa Samson Siasia shiga harkokin wasa har abada, kociyan wanda ya jagoranci tawagar Najeriya a wasannin Olympic inda har suka yi nasarar lashe lambobin yabo har a karo biyu, bayan samunsa da laifin sayar da wasa.

FIFA ta ce, Siasia ya amince cewar ya karbi na goro da nufin sauya sakamakon wasa.

Sai dai hukumar ta FIFA ba ta fayyace takamamman wasannin da take binciken ba amma ta ci tarar Siasia kudin Swiss francs 50,000, kwatankwacin dalar Amurka 50,000.

Siasia ya taba zama kociyan Najeriya daga watan Disambar 2010 zuwa Oktoban 2011, kana ya sake zama kociyan a shekarar 2016 a lokacin da ya jagoranci tawagae 'yan wasan 'yan kasa da shekaru 23 a gasar Olympics ta 2016 inda suka doke Honduras da 3-2 suka lashe lambar yabo ta tagulla. Kana ya taba jagorancin tawagar Najeriyar inda ta lashe lambar azurfa a gasar Olympics ta Beijing a 2008. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China