Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hadarin kwale-kwale a Nijeriya ya karu zuwa 5
2019-08-16 10:38:56        cri
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hatsarin kwale-kwale a jihar Lagos na Nijeriya, ya karu zuwa 5 da safiyar jiya Alhamis, bayan masu ceto sun gano gawarwaki 2 a cikin ruwa.

A cewar shugaban hukumar kula da sufuri ta ruwa na jihar Lagos, Oluwadamilola Emmanuel, kwale-kwalen guda biyu na dauke da mutane 18 a lokacin da suka yi taho mu gama da yammacin ranar Talata, a kogin Irewe dake yankin karamar hukumar Ojo ta jihar.

Da farko yayin aikin ceto, an gano gawarwakin mutane 3, yayin da aka ceto mutane 13 da ransu.

An kuma gano gawarwakin ragowar mutanen da a baya aka ayyana bacewarsu, inda aka kawo karshen aikin ceton.

Binciken farko farko da hukumar ta gudanar, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne saboda tukin ganganci da gudu da direbobin ke yi.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China