Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya da Kamaru sun amince su bunkasa hadin gwiwa a fannin yaki da ta'addanci a kan iyakarsu
2019-07-06 14:55:20        cri
Kasashen Kamaru da Nijeriya, sun amince da kara daukar matakan bunkasa hadin gwiwarsu a bangarori da dama, da zummar yaki da ta'adannci a kan iyakokinsu.

An cimma matsayar ce jiya da daddare, bayan kammala taro karo na 7, na kwamitin kula da tsaron iyakokin Kamaru da Nijeriya da aka shafe yini 2 ana yi a birnin Yaounden Kamaru.

Jami'ai mahalarta taron, sun amince da musayar bayanai a kai a kai, da nufin dakile ayyukan ta'addanci, ciki har da hare-haren BH da na 'yan aware da hakar ma'adinai da safarar makamai da miyagun kwayoyi ta haramtattun hanyoyi tsakanin iyakokinsu.

An kafa kwamiti mai kula da tsaron iyakar Nijeriya da Kamaru ne a shekarar 2012 a Nijeriya, da nufin karfafa tsaro a kan iyakar kasashen biyu. An gudanar da taron kwamitin karo na 6 a shekarar 2018, a Abuja, babban birnin Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China