Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Beijing ta samun ci gaba sosai ta fuskar kirkire-kikire a fannin kimiyya da fasaha
2019-08-23 11:25:06        cri
A matsayin cibiyar kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, birnin Beijing ya kai matsayi na farko a fannoni daban-daban a cikin shekaru 70 da suka gabata ta sha'anin kimiya.

Da yammacin jiya Alhamis, mataimakin direktan kwamiti mai kula da kimiyya da fasaha na birnin Beijing Yang Renquan, ya shedawa manema labarai cewa, sakamakon da aka bayar karo na biyar kan kiyasin makomar kimiyyar kasar Sin ya bayyana cewa, ci gaban kimiyya da fasaha dake sahun gaba a duniya da Sin ta samu, birnin Beijing ya mallaki kashi 55.7 cikin dari, matakin da ya baiwa kasar goyon baya matuka a fannin tsaro, da bunkasuwar tattalin arziki, da ci gaban al'umma, da kyautata zaman rayuwar jama'a.

Yang Renquan ya yi bayanin cewa, a cikin wadannan sana'o'i masu alaka da kimiya da fasahar zamani, sha'anin kiwo lafiya da samar da magunguna na birnin Beijing, ya samun moriya kudin Sin RMB biliyan 186.76, adadin da ya karu da kashi 14.3 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara.

Ban da wannan kuma, yawan kudin dake shafar sha'anin na'urori masu sarrafa kansu da kansu ya kai RMB biliyan 150. Kaza lika Yawan motoci masu amfani da lantarki da Beijing ke da su ya kai dubu 284.7 wanda ya kai matsayin farko a kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China