Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu kyautatuwar muhallin halittu yayin da ake kara inganta kare dazuzzuka
2019-08-22 09:21:39        cri

Mataimakin darakta a ma'aikatar gandun daji da kula da yankunan tsarrai na kasar Sin Li Shuming, ya ce Sin ta samu manyan nasarori a fannin kare gandun daji cikin shekaru 20 da suka gabata.

Li ya bayyana hakan ne yayin wani taron karawa juna sani, yana mai cewa fadin gandun dajin kasar ya karu da kusan hekta miliyan 28.53, kana albarkatun gandun dajin sun samar da moriya ta kusan kubik mita biliyan 3.78.

Jami'in ya ce gandun daji na ainihi, wanda ke wakiltar kaso mafi tsoka na gandun dajin kasar, ya taka muhimmiyar rawa wajen fadada yankunan dazukan dake kasar, inda yawan sa ya kusa ninkawa daga kaso 12 bisa dari a shekarar 1980, zuwa kaso 22.96 bisa dari ya zuwa karshen shekarar da ta gabata.

Li Shuming ya ce, gandun daji na ainihi na fuskantar mamaya, sai dai mahukuntan kasar na daukar matakai domin kare martabar wadannan dazuka. Ya ce za a tabbatar da hana sare bishiyoyi domin kara farfado da dazukan kasar, yayin da ake daukar matakan kimiyya domin kyautata yanayin dazukan.

Mahukuntan kasar Sin na hasashen nan da shekarar 2035, fadin dazukan kasar na ainihi zai daidaita, inda zai kai fadin hekta miliyan 200, a wani mataki na cimma burin gina Sin mai kayatarwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China