Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 3 sun rasu wasu 2 kuma sun bace sakamakon hadarin jirgin ruwa a jihar Lagos
2019-08-14 19:59:48        cri
Mahukunta a jihar Lagos dake kudancin Najeriya, sun tabbatar da rasuwar mutane 3, da wasu 2 kuma da suka bace, sakamakon hadarin wasu jiragen ruwa 2 da ya auku a jiya Talata.

Jami'in hukumar dake kula da hanyoyin ruwa a jihar Oluwadamilola Emmanuel, ya shaidawa manema labarai cewa, jiragen ruwan dakon fasinjoji 18 ne suka yi karo da juna, a yankin Irewe dake karamar hukumar Ojo.

Ya ce binciken farko ya tabbatar da cewa, hadarin ya auku ne sakamakon tukin ganganci, da kuma gudun da ya wuce kima da matukan jiragen ke yi lokacin da hadarin ya auku. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China