Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar 'yan wasan kwallon kafan Najeriya 'yan kasa da shekaru 17 sun fara samun horo a Abuja
2019-08-15 09:32:56        cri
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ta gayyaci 'yan wasa 52 zuwa sansanin samun horo dake Abuja, babban birnin kasar, a shirye-shiryen kasar na halartar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 'yan kasa da shekaru 17.

Mai magana da yawun hukumar Ademola Olajire, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, galibin'yan wasan da aka gayyata, sun riga sun iso sansanin samun horon, karkashin kulawar kociyan tawagar Manu Garba, wanda ya jagoranci tawagar 'yan wasan Najeriyar da ta lashe kofin a karo na hudu a gasar da aka buga a hadaddiyar daular Larabawa a shekarar 2013.

A baya dai 'yan wasan na Golden Easglets sun lashe kofin a shekarar 1985, 1993 da 2007 da kuma shekarar 2015.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China