Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin a MDD ya nemi a kiyaye ikon kasashe da ake fama da rikici game da batun hakkin yara
2019-08-03 15:58:39        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya ce game da batun kare hakkin kananan yara a kasashen da ake fama da hare haren 'yan bindiga, tilas ne kasashen da abin ya shafa su yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu kuma wajibi ne a girmama shugabancin kasashen.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya nuna damuwa game da yawan yaran da suka mutu a hare haren kungiyoyin masu dauke da makamai a shekarar da ta gabata, inda sama da kananan yara 12,000 aka hallaka da kuma jikkatawa a cewar rahoton MDD.

A yayin taron kwamitin sulhun MDD, wakilin kasar Sin ya ce ya kamata al'ummar kasa da kasa su tallafawa kasashen da matsalar ta shafa wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu wajen kare kananan yara daga hare haren masu dauke da makamai.

Ya ce babban muhimmin al'amari game da aiwatar da kudurin da kwamitin sulhun MDDr ya cimma game da kare hakkin yara ya dogara ne kan irin kokari da kuma hadin gwiwar da gwamnatoci ke yi wajen warware matsalar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China