Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na matukar adawa da karin harajin Amurka kan hajojinta
2019-08-02 19:41:23        cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana rashin amincewa da aniyar Amurka, ta kara wa hajojin Sin da ake shigarwa kasar harajin kaso 10 bisa dari.

Ma'aikatar ta ce Amurka na shirin kakaba sabon haraji kan hajojin Sin da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 300, amma ko shakka ba bu Sin za ta dauki matakan kare hakkokin ta.

Kakakin ma'aikatar ya bayyana cewa, matakin na Amurka, wanda ka iya habaka takaddamar sassan biyu bai dace da moriyar al'ummun su, da ma sauran kasashen duniya ba, zai kuma yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya baki daya.

Jami'in ya kara da cewa, har kullum Sin na da imanin ba wanda zai ci riba daga yakin cinikayya, amma kuma ba ta tsoronsa. Don haka dai Sin za ta mayar da martani idan har bukatar hakan ta kama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China