Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Sin sun dakatar da sayen amfanin gona daga Amurka
2019-08-06 09:52:17        cri
Hukumar samar da ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta Sin, da ma'aikatar cinikayyar kasar, sun ce kamfanonin kasar su dakatar da sayo kayayyakin amfanin gona daga Amurka, kana kasar na iya karawa hajojin Amurka da ake shigarwa Sin bayan ranar 3 ga watan Agustan nan haraji.

Wannan dai mataki na zuwa ne, bayan da Amurka ta ayyana karawa hajojin Sin da ake shigarwa Amurka harajin kaso 10 bisa dari, hajojin da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 300, matakin da Sin ke cewa ya keta hurumin matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a birnin Osaka na kasar Japan.

Wata majiya ta gwamnati ta bayyana cewa, a matsayin ta na kasa mai yawan al'umma, Sin muhalli ne dake karbar tarin hajojin amfanin gona daga Amurka, don haka fatan da ake yi shi ne, mahukuntan ta za su aiwatar da matsaya da aka cimma a Osaka bisa sahihiyar zuciya, su kuma rungumi matakan cika alkawarin su, na samar da kyakkyawan yanayin aiwatar da hadin gwiwa a fannin harkokin gona. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China