Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin kawar da talauci da samar da ci gaba da kuma kare muhalli
2019-08-23 10:43:11        cri

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin kawar da talauci da samar da ingantaccen ci gaba da kiyaye muhalli da kuma inganta zaman takewar jama'a.

Xi Jinping, wanda shi ne Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne lokacin da yake rangadi a lardin Gansu, dake arewa maso yammacin kasar Sin, daga ranar Litinin zuwa jiya Alhamis.

Yayin rangadin, shugaba Xi, ya yi kira da a kara kirkire-kirkire da kwarin gwiwa da gudanar da managartan ayyuka da hadin kai, don ci gaban lardin Gansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China