Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci da a kara azama wajen raya aladun kasar Sin
2019-08-20 11:11:19        cri

Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya bukaci masana da kwararru, da su kara azama wajen kare al'adun kasar Sin.

Xi Jinping ya yi wannan kira ne a jiya Litinin, yayin taron musayar ra'ayi da ya gudana a garin Dunhuang, inda ya bukaci masana da wakilain sassan hukumomin raya al'adu, da su himmatu wajen cimma wannan muhimmin buri.

Xi wanda ke ziyarar aiki a lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin, ya jaddada muhimmancin hada gwiwar bunkasawa, da yayata al'adun gargajiyar kasar Sin. Kaza lika ya yi kira da a kara azama, wajen aiwatar da musayar tsakanin kasar sa da sauran kasashen duniya, a kuma yi koyi da managartan nasarorin da sauran kasashe, da yankunan duniya suka cimma.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China