Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya kai ziyara lardin Gansu
2019-08-21 20:23:37        cri

Yau ne Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS kuma shugaban kasar Sin ya ziyarci wani sabon gari dake yankin Gulang da yankin gandun daji na lardin Gansu dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin.

An dai tsugunar da mazauna sabon garin Gulang ne, inda suka samun rayuwa mai inganci bayan fita daga kangin talauci.

Bugu da kari, Xi ya duba shirin dasa itatuwa dake gudana a yankin hamada na Gansu, inda ya kalli sabbin ci gaban da aka samu a fannin yaki da hamada da kare muhalli.(Ibrahim)

 

 

 

 

 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China