Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya bukaci Amurka ta guji lalata dangantakar dake tsakaninsu
2019-05-19 20:22:08        cri
Mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bukaci Amurka da ta yi kaffa-kaffa a yunkurin da take na neman lalata moriyar kasar Sin, Wang ya bayyana hakan ne a hirarsa da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ta wayar tarho.

Yana mai cewa, a baya bayan nan, Amurka ta dauki wasu matakai wadanda za su yi matukar illa ga moriyar kasar Sin a dukkan fannoni, ciki har da matakin Amurkar na kawo illa ga wasu kamfanonin kasar Sin game da ayyukansu na yau da kullum, ta hanyar daukan matakan siyasa, mista Wang ya ce, kasar Sin ta yi Allah wadai da babbar murya kan daukar irin wadannan matakai da bangaren Amukar ta yi.

"Muna gargadin Amurka da ta yi taka-tsan-tsan," Wang ya fadawa Pompeo, ya kara da cewa, ya kamata Amurka ta canza salonta ba tare da bata lokaci ba domin kaucewa lalata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wang Yi ya ce, tarihi da abin da ke faruwa a zahiri sun nuna cewa, a matsayinsu na manyan kasashe biyu, Sin da Amurka dukkansu suna amfana daga hadin gwiwar dake tsakaninsu kuma za su iya tafka mummunar hasara daga takaddamar dake wanzuwa a tsakaninsu. Mr. Wang ya kara da cewa, hadin gwiwa shi ne kadai abin da ya fi dacewa da kasashen biyu.

Sannan ministan harkokin wajen na Sin ya nuna cewa, ya kamata bangarorin biyu su bi umarnin da shugannin kasashen suka tsara, su yi watsi da banbancin dake tsakaninsu bisa tushen girmama juna, kuma su fadada hadin gwiwarsu bisa moriyar juna, kana su yi aiki tukuru wajen ingiza matsayin dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Amurka ta hanyar tuntubar juna, da hadin gwiwa cikin lumana. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China