Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sanda a Najeriya sun cafke wasu bata gari 79 a arewacin kasar
2019-08-08 10:00:20        cri

Rundunar 'yan sanda a tarayyar Najeriya, ta ce ta samu nasarar damke wasu bata gari da yawansu ya kai 79, ciki hadda 'yan fashin shanu, da masu garkuwa da mutane, da sauran wadanda ake zargi da aikata laifuka daban daban, sakamakon wani samame da jami'an rundunar suka gudanar a jihar Kaduna dake arewacin kasar

Kakakin rundunar na jihar ta Kaduna Ali Janga, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an cafke wadanda ake zargin ne a garin Rijana, dake kan hanyar Kaduna zuwa birnin Abuja, da kuma wasu sassa daban daban na jihar. Kaza lika an samu nasarar karbe bindigogi 35, da kuma shanu 439.

Janga ya ce yanzu haka rundunar 'yan sandan na gudanar da kwaskwarima ga tsarinta na tura jami'an tsaro, musamman a sassan babbar hanyar mota ta Kaduna zuwa Abuja, da Kaduna zuwa Zaria, da Kaduna zuwa birnin Gwari, da nufin tabbatar da tsaro ga matafiya.

A baya-bayan nan dai an sha fama da ayyukan masu satar mutane a sassan Najeriya, inda har ma a watan Mayun da ya gabata, yayin wani taro game da tsaro da ya gudana a Kaduna, babban sifeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu, ya tabbatar da cewa, a kalla mutane 685 ne aka yi garkuwa da su, a watanni hudun farko na shekarar bana.

A ranar Litinin din farkon makon nan ma, sai da wasu gungun 'yan bindiga suka hallaka wani malamin majami'a, a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Kana suka yi garkuwa da mai dakinsa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China