Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Xi da Putin sun jagoranci kulla huldar dangantaka a sabon zamani don raya cigaban kasa da kasa
2019-06-08 17:12:15        cri

Ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai zuwa Rasha ta nuna alamun kara zurfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu, hakan na nuna da cewar mu'amalar ta kafu daram, kana kasar Sin ta yi amanna cewa mu'amalar kasashen biyu ta cin moriyar juna ce wacce babu abin da ke iya girgiza ta, mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi shi ne ya bayyana hakan a jiya Juma'a.

A ranar Juma'a shugaba Xi ya kammala ziyarar aikinsa ta kwanaki 3 a kasar Rasha, a lokacin ziyarar ya halarci taron dandalin tattalin azriki na St.Petersburg (SPIEF) karo na 23. Haka zalika a lokacin ziyarar shugaban kasar ta Sin ya ziyarci wasu muhimman ayyuka kusan 20 a Moscow da birnin St.Petersburg, wadanda suka bada kyakkyawan sakamako, inji Wang.

A matsayin wata gagarumar nasara ta fuskar siyasa da aka cimma a lokacin ziyarar, shugaba Xi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan sanarwar daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha zuwa matsayin cikakkiyar dangantaka a sabon zamanin da muke ciki.

Dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta kasance a matsayin muhimmiyar alaka wacce ta kai matsayin dangantakar koli, matakin dake zama ginshiki wajen tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa da kasa, in ji Wang.

A lokacin ziyarar tasa, shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi a taron dandalin tattalin arzikin St.Petersburg wanda ya kasance a matsayin muhimmin dandali ga al'ummar kasa da kasa wanda zai ba su damar yin musayar ra'ayoyin game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Xi ya bayyana dauwamamman cigaba a matsayin muhimmin al'amarin da zai warware matsalolin duniya, kuma a matsayin hanya mafi dacewa da za ta kara hadin gwiwar kasa da kasa don cimma buri iri daya a tsakanin kasa da kasa, in ji Wang.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China