Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin FedEx ya amince da kuskuren da ya yi wajen jigilar kayan kamfanin Huawei
2019-05-28 20:46:09        cri
Kamfanin aikewa da sakwanni na Amurka mai suna FedEx reshen kasar Sin ya bayar da wata sanarwa a yau Talata, inda ya amince cewa ya yi kuskure wajen jigilar wasu kayan kamfanin sadarwar kasar Sin wato Huawei. Haka kuma a wannan rana, kamfanin Huawei ya gabatar da korafi ga hukumar kula da harkokin gidajen waya ta kasar Sin. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, kamfanin Huawei na sake nazarin dangantakar dake tsakaninsa da kamfanin FedEx.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, a kwanakin baya ne kamfanin FedEx ya aike da wasu kayan kamfanin Huawei guda biyu daga Japan zuwa Amurka, wadanda da ma aka shirya aika su Sin daga Japan, matakin da kamfanin Huawei ya yi Allah-wadai da shi. Tun farkon dai, kamfanin FedEx ya karyata wannan labari a shafinsa na sada zumunta na Weibo, inda ya ce labarin da ake yadawa a Intanet karya ce tsagwaronta.

Masu amfani da Intanet na kasar Sin na ganin cewa, da gangan kamfanin FedEx ya yi wannan kuskure, kuma da wuya a gaskata abin da kamfanin FedEx ya fada.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China