Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta bayar da gargadi game da cutar Ebola
2019-06-13 11:11:50        cri
A jiya Laraba gwamnatin kasar Kenya ta bada gargadi game da kiwon lafiya a sakamakon samun rahoton bullar annobar cutar Ebola (EVD) a makwabciyar kasar Uganda.

Sicily Kariuki, sakatariyar hukumar lafiyar kasar, tce Kenya ta baza dukkan jami'anta a dukkan yankunan da ake da fargabar yiwuwar bullar annabor cutar domin dakile ta.

Jamai'ar ta bayyana cewa, tuni gwamnatin kasar ta fara aikin tantance dukkan bakin da suka shigo kasar daga kasashen jamhuriyar dimokuradiyyar Kongo, Uganda, da sauran makwabtan kasashe inda ake amfani da na'urar zamani ta auna yanayin zafin jiki a babban filin jirgin saman kasar da sauran tashoshin ruwa dake kasar.

Kenya ta dauki wadannan matakai ne bayan samun rahoton bullar cutar ta Ebola a Uganda, inda aka kebance wani karamin yaro dan shekaru 5 bayan da aka bada rahoton shi da mahaifiyarsa sun taho daga kasar Kongo inda suka isa Uganda a ranar Litinin ta wannan makon.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China