Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin MDD sun yi kira da a hada hannu don kawo karshen Ebola a DRC
2019-08-01 13:33:41        cri
Shugabannin hukumomin MDD da dama sun yi kira da a hada hannu, wajen ganin bayan cutar Ebola da ta barke a Jamhuriyar demokirdaiyar Congo(DRC) gabanin cika shekara guda da ayyna barkewar cutar a kasar ..

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus da mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai da tsare-tsare ayyukan agajin gaggawa Mark Lowcook, da darektan UNICEF Henrietta Fore da takwaransa na shirin samar da abinci da aikin gona na duniya David Beasley ne, suka yi wannan kiran cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar. Inda suka bayyana kudirinsu na hada kai da al'ummar DRC, da mika ta'aziya ga wadanda cutar ta halaka, tare da kiran da a yi kokarin hada karfi da karfe don ganin bayan wannan cuta.

Yau 1 ga watan Agusta ne, ake cika shekara guda da gwamnatin jamhuriyar demokiradiyar Congo ta ayyana barkewar kwayar cutar Ebola a lardin arewacin Kivu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China