Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 2 sun mutu 5 sun jikkata a hadarin mota a wani babban titin Najeriya
2019-08-12 11:05:42        cri
Mutane biyu sun mutu kana wasu mutanen biyar sun samu raunuka a sakamakon wani hadari inda wata mota ta bi ta kan wani babur a yankin Olowotedo dake garin Mowe a jahar Ogun dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.

Clement Oladele, babban jami'in hukumar kiyaye haddura ta jahar Ogun ya ce, hadarin ya faru ne a ranar Asabar a babbar hanyar motar Ibadan zuwa Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Oladele ya fadawa manema labarai cewa, mutane 8 ne hadarin ya rutsa da su lamarin da ya haddasa hasarar rayukan mutane biyu.

Ya ce tuni aka garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti don ba su kulawa.

Jami'in ya shawarci masu ababen hawa da su yi kaffa-kaffa kuma su guji gudun da ya wuce kima, musamman a sassan da ake gudanar da aikin gyaran hanyar, domin kaucewa hasarar rayuka da dukiyoyi.

Ana yawan samun hasarar rayuka a sakamakon hadarin mota a Najeriya, galibi saboda rashin kyawun hanyoyin mota ko saboda tukin ganganci da daukar kayayyakin da suka wuce kima.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China