Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kasashen Afrika su hada kansu yayin taron kolin sauyin yanayi na duniya dake tafe
2019-08-19 11:34:52        cri

Hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), ta bukaci kasashen Afrika da su yi magana da murya guda game da matsayar nahiyar a yayin taron koli na kasa da kasa kan batun sauyin yanayi, wanda aka shirya gudanarwa a watan gobe, babban sakataren MDD Antonio Guterres shi zai jagoranci taron.

A yayin da ake tsaka da yin kiraye-kirayen neman lalubo cikakkiyar hanyar yaki da matsalar sauyin yanayi a duniya, hukumar ECA ta bayyana cewa, tana shirin gudanar da wani babban taron nahiyar Afrika game da batun sauyin yanayi da raya cigaban Afrika wato (CCDA), wanda za ta gudanar a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga watan Agusta, mai taken "Daukar matakan tunkarar matsalar sauyin yanayi don raya tattalin arzikin Afrika".

A cewar James Murombedzi, babban jami'in cibiyar tsara dabarun yaki da sauyin yanayi na Afrika (ACPC) karkashin hukumar ECA, ya ce, babban taron nahiyar wanda zai gudana a hedkwatar kungiyar tarayyar Afrika AU, zai taimakawa Afrikan wajen fito da matsaya guda da nahiyar za ta dauka a lokacin taron kolin sauyin yanayin na kasa da kasa dake tafe.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China