Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi kira ga kasashen Afirka da su hanzarta aiwatar da yarjeniyoyin sauyin yanayi
2019-08-13 11:00:44        cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) a takaice, ta yi kira ga kasashe mambobinta, da su hanzarta aiwatar da dukkan yarjeniyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya kan matsalar sauyin yanayi da suka sanyawa hannu, don magance tasirin da wannan matsala ta haifar.

Wannan kira na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar zaman lafiya da tsaron kungiyar AU ta fitar a ranar Litinin, bayan ganawar hukumar ta baya-bayan da ta gudana a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababan kasar Habasha, bisa taken "Bala'u daga indallahi da sauran bala'u a Afirkaļ¼šLamarin da ya wuce sanin kowa".

Sanarwar ta bayyana cewa, bala'u daga indallahi gami da matsalar sauyin yanayi, sun kara ta'azzara halin da al'ummomi ke ciki, da haifar da barazana ga muhimman albarkatun da ake da su, da ma yadda ake cin gajiyarsu.

Alkaluma da kungiyar ta fitar sun nuna cewa, kimanin kaso 90 cikin 100 na bala'un dake faruwa a kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara, suna da nasaba da yanayi da sauyin yanayi, wadda daga karshe ke shafar kaso 10 zuwa 20 na tattalin arzikin kasashen.

Don haka, sanarwar ta ce, akwai bukatar kasashe mambobin kungiyar AU, da su kara daukar managartan matakan magance tasirin matsalar sauyin yanayi, lalacewar muhalli, da bala'u daga indallahi.

Bugu da kari, hukumar ta sake yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka, da su ba da muhimmanci kan matakan magance sauyin yanayi a yankunan da tashin hankali ya shafa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China