in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nahiyar Afrika ta bukaci kasashen da suka ci gaba, su martaba alkawarin da suka yi na bada dala biliyan 100 na tunkarar sauyin yanayi
2019-03-20 10:09:30 cri

Tarayyar Afrika AU, ta yi kira ga kasashen da suka ci gaba, su martaba alkawarin da suka yi na tara dala biliyan 100 duk shekara, domin tallafawa shawo kan matsalolin sauyin yanayi da matakan tunkararsu a kasashe masu tasowa.

Da take kiran a madadin Tarayyar, yayin zaman da aka yi na makon sauyin yanayi a ranar Litinin, babbar jami'ar tsara manufofi ta hukumar AU Olusola Olayide, ta ce samun kudin na da muhimmanci matuka ga nasarar nahiyar Afrika ta tunkarar matsalolin sauyin yanayi.

Ta ce kasashen Afrika 48 ne suka amince da aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris. A don haka take kira ga kasashen da suka ci gaba, su rika bada dala biliyan 100 da suka yi alkawari a kowacce shekara ya zuwa shekarar 2020.

Olusola Olayide, ta kara da cewa, Afrika na matukar bukatar kudin tunkarar sauyin yanayi da horo da kirkiro fasahohi domin magance matsalar wadda ita ce babban burin nahiyar, da kuma samar da tsarin aikin gona mai jure matsalar.

Ta kuma jadadda cewa, shugabancin AU ya kuduri niyyar aiwatar da yarjejniyar birnin Paris tare da daukar matakan cimma muradun ci gaba masu dorewa ya zuwa 2030 da kuma ajandar da nahiyar ke son cimmawa ya zuwa 2063. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China