Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya bada muhimmin umarni ga ayyukan raba ire-iren abubuwan shara
2019-06-03 13:59:29        cri
Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada wani muhimmin umarni ga ayyukan raba ire-iren abubuwan shara na kasar, inda ya jaddada cewa, ayyukan na da nasaba da muhallin zaman rayuwar jama'a, da tsimin makamashi, kuma alama ce ta matsayin wayewar kan al'umma.

Baya ga haka, Xi ya nuna cewa, ya kamata a sanya jama'a su fahimci muhimmanci da wajibcin ayyukan raba ire-iren abubuwan shara, kuma ta hanyar kokarin ba da jagoranci ne za'a taimakawa jama'a su yi kokari tare don kyautata muhallin zaman rayuwa, da taka muhimmiyar rawa wajen samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da samun dauwamamman ci gaba a kasar ta Sin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China