An gudanar da taron ranar rage fitar da sinadarin carbon na shekarar 2019 a birnin Beijing

Ranar 19 ga wannan wata rana ce ta rage fitar da sinadarin carbon ta kasar Sin karo na 7 ce. A wannan rana da safe, hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing ta gudanar da bikin fadakar da rage fitar da sinadarin carbon ta shekarar 2019, inda masana masu kula da tinkarar sauyin yanayi da gurbata yanayin iska suka tattauna da gabatar da kiran Beijing na rage fitar da sinadarin carbon na shekarar 2019. (Zainab)