Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samar da ban dakuna 30,000 domin amfanin masu yawon shakatawa a shekarar 2018
2019-06-17 10:47:22        cri
Ma'aikatar raya al'adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta ce gwamnatin Sin ta kakkafa da gyarawa da kuma inganta ban dakuna kimanin 30,000 cikin shekara guda da rabi domin amfanin masu yawon shakatawa.

Adadin ya kai kaso 47 bisa 100 na shirin da aka tsara na shekaru 3 wanda gwamnati ta bayyana, kamar yadda ma'aikatar raya al'adun ta fitar.

Domin bunkasa harkokin yawon shakawa na cikin gida, kasar Sin ta sha alwashin daga matsayin ban dakuna kimanin 64,000 tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020, don amfanin masu yawon shakatawa, kamar yadda aka tsara.

Tun bayan da aka kaddamar da shirin yin garambawul ga ban dakuna a shekarar 2015 domin kara adadin yawansu da kuma tsaftar ban dakunan a cibiyoyin yawon shakatawa, kasar Sin ta samu kyautatuwar al'amurra ta fuskar inganci da kuma yawan ban dakunan wuraren yawon shakatawa, sakamakon yadda aka dora muhimmanci wajen kulawa da ban dakunan, in ji ma'aikatar raya al'adun ta kasar Sin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China