Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Biranen kasar Sin sun samu karuwar kyautatuwar iska
2019-07-09 11:01:25        cri
Ma'aikatar kula da muhallin halittu da sauran yankunan muhalli ta kasar Sin ko MEE a takaice, ta ce da yawa daga biranen kasar sun samu karin kyautatuwar iska a watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2019, a gabar da mahukuntan kasar ke aiwatar da karin matakai na kare muhalli.

Ma'aikatar ta ce a birane 337 da ta nazarta, matsakaicin kyawun iskar su ya kai kaso 80.1 bisa dari cikin watannin 6, wanda hakan ke nuna karuwar ingancin iskar da kaso 0.4 a shekara guda.

Kaza lika alkaluman da MEEn ta fitar a jiya Litinin, sun nuna cewa, matsakaicin karuwar awon gurbatar iska na PM2.5 da aka samu a biranen ya ragu, da kaso 2.4 bisa dari a shekara guda, wanda a tsakanin lokacin bai wuce "micrograms 40" a kan kowace "cubic meter" ba. Yayin da kuma yawan matsakaicin sinadarin "sulfur dioxide" da PM10 dake cikin iska suka yi kasa, zuwa kaso 4.2 da kaso 14.3 bisa dari.

An danganta kyautatuwar iska a biranen ne, da namijin aikin da gwamnati ke yi a fannin yaki da gurbatar iska da lalacewar muhalli.

A wani ci gaban kuma, ma'aikatar kare muhallin ta alkawarta sake kaddamar da zagaye na gaba, na sanya ido kan ingancin muhalli, wanda karkashinsa, masu aikin sanya ido za su ziyarci larduna 6, tare kuma da wasu manyan kamfanoni biyu, dake karkashin kulawar gwamnatin tsakiyar kasar. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China