Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Hainan dake kudancin kasar Sin zai fara aiwatar da aikin tantance bola a badi
2019-06-17 10:23:24        cri

Sashen kula da samar da gidaje da raya birane da kauyuka na lardin tsibiri na Hainan dake kudancin kasar Sin, ya ce lardin ya kammala shirya tsarin tantance bola a shekarar 2020.

A cewar sashen, tsarin ya kunshi manufofi da hakkokin bangarori masu ruwa da tsaki da bukatun tantance bola.

Shirin na da nufin sake juya kaso 35 na bolar da ake samarwa a lardin ya zuwa shekarar 2021.

A yanzu, lardin na amfani ne da dabarun cike filaye da kone bola a matsayin hanyoyin kawar da shara.

Kawo yanzu, an gina wuraren zubar da bola 21 a Hainan, ciki har da na cike filaye 16 da cibiyoyi 5 na samar da lantarki daga zafin bolar da ake konawa. Sannan an gina wuraren da ake saukewa da kwasar bola 250 da wuraren tattara su 12,500.

An kafa wani hadadden tsarin kawar da bola a lardin, inda kaso 95 na kauyukan lardin ke da kayayyakin tattarawa da jigilar bola, yayin da masu aikin tsaftace muhalli a kauyukan suka kai 19,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China