Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin HKSAR ta fidda sanarwar dake goyon bayan 'yan sanda su dauki tsauraran matakai
2019-08-18 16:22:41        cri

Kakakin gwamnatin yankin musamman na Hong Kong (HKSAR), ya fitar da sanarwa a ranar 18 ga wata dake bayyana yin Allah wadai da zanga zangar da wasu kungiyoyi ke gudanarwa mai taken kai hari kan 'yan sanda, sanarwar ta jaddada cikakken goyon bayan gwamnatin HKSAR ga 'yan sanda da su dauki tsauraran matakan tabbatar da doka da oda, kana ta mika godiya ga dukkan jami'an 'yan sanda bisa namijin kokarinsu wajen kokarin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma zakulo wadanda suka keta doka don gurfanar da su gaban shari'a.

Kakakin yace, a ko da yaushe Hong Kong ya kasance birni ne mai cikakken zaman lafiya. Adadin laifukan da aka samu a birnin a shekarar 2018 ya yi matukar raguwa tun daga shekarar 1974, kuma adadin laifukan da aka samu cikin adadin mutane 100,000 shi ne mafi karanci tun daga shekarar 1970. Sai dai abin takaici, bayan jerin gwanon zanga zanga da bore da wasu kungiyoyin suka kaddamar cikin watanni biyun da suka gabata, an samu tsananin hare hare da aka dinga kaiwa jami'an 'yan sanda da muggan makamai, wanda adadin hare haren ya kai 75, da lalata wasu daga cikin ofisoshin 'yan sandan. Kawo yanzu, masu zanga zangar sun raunata jami'an 'yan sanda kimanin 180.

Kakakin gwamnatin HKSAR yace, gwamnati ta amince jama'ar su gudanar zanga zangar lumana domin bayyana damuwarsu, kana tana jaddada yin kira ga wadanda suke gudanar da zanga zangar cewar su tabbatar sun gudanar da gangamin cikin lumana da nuna dattaku, kuma su gujewa tashin hankali, domin a samu nasarar maido da zaman lafiya a birnin Hong Kong nan bada jimawa ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China